View the h-hausa Discussion Logs by month
View the Prior Message in h-hausa's December 2004 logs by: [date] [author] [thread] View the Next Message in h-hausa's December 2004 logs by: [date] [author] [thread] Visit the h-hausa home page.
Malama Suyetina, Gaisuwa mai yawa da fatan alheri. Na ga tambayar da ki ka yi ta hanyar H-Hausa. Na ji dadin jin cewar har yanzu jaridar Gaskiya ta fi Kwabo ta na nan. Hausawa na yin amfani da karin maganar "kan mage ya waye" domin su fahintar da ma su sauraro ko kuma wanda a ke nufi ya/ta fahimtu da cewa jama'ar ko kuma mutumin/mutuniyar da ba a zaton sun/ya/ta kai wani fagen wayewa to ya ma fice haka. Da a ka ce wai kauyawa ma sun ki kai kudin su ajiya a banki, a na nufin sun gane cewa banki ba koda yaushe ya ke kasancewa cikin sukunin bayar da ajiyar da a ka saka a cikn sa ba. Idan kin tuna bankunan Nigeria da yawa a 'yan shekarun baya sun shiga matsayi mai rudarwa domin sun durkushe kuma duk wandan da su ka saka kudin su a cikin bankunan sai asarar su su ka yi; domin hukuma ba ta tsaya ba wajen bin hakkin su ba saboda wai akwai gidan inshora (Nigeria Deposit Insurance Company) wanda ya ke da kayadajjen kima wajen biyan kudin da ma su ajiya suka zuba a bankin da ya durkushe. Domin haka ne su kauyawa su ka duba cewa ai ba sai a banki ba kadai za a iya ajiyar kudi ba, koda ya ke akwai hatsari tattare da ajiyar makudan kudi a gida (musamman a karkashin gado ko cikin tukwane!). A bisa ga dan bayanin da na ke gani "kan mage ya waye" a nan ya na nufin bankuna ba za su yiwa kauyawa wayo ba ko kuma romon baka domin su zuba kudin su domin ajiya, asali ma dai ai sai mutum ya iya turanci zai iya rubuta cheque domin diban kudin sa a banki domin kuwa bankuna ba sa yin amfani da ajami ko kuma Hausar boko. Kin ga kuwa ina a ka ga rufin asiri? Ka/kya kai kudin ka/ki wajen da sai an turanci za a debo? Kai a gaskiya "kan mage ya waye" in dai hukuma ba za ta sauya yadda bankuna su ke tafiyar da harkokin su ba domin sauran mutanen kauye su gane. I na fatan wannan dan jawabi zai gamsar da ke. Ki huta lafiya. -- Ibrahim Hamza Ph.D. Candidate Department of History York University 4700 Keele Street Toronto, ON Canada M3J 1P3 -- Wannan wasik'ar i-mel ce daga H-Hausa, inda za'a cigaba da hira game da harshe da al'adu da tarihi da sauran lamura na Hausawa da mak'wabtansu.
|